5 Mayu 2021 - 14:40
Najeriya: Sojoji Sun Nisanta Kansu Daga Duk Wani Yunkuri Da Zai Ga Hambarar Da Buhari

Rundunar ta bayyana haka ne bayan da wasu fitattun ‘yan siyasa kuma daga jam’iyyun adawa na kasar suka bukaci sojojin Najeriya su kwace mulki daga hannun Buhari domin kawo karshen matsalolin tsaro wadanda suka addabi kasar.

ABNA24 : Matsalolin tsaro a Najeriya dai, sun hada da Boko Haram a raewa maso gabacin kasar, da masu satar mutanen don karban kudaden Fanta a arewa masu gabacin kasar, da kuma yan aware na kungiyar Ibo daga kudu maso gabacin kasar.

Brigadier General Onyema Nwachukwu, daraktan riko a bangaren watsa labarai na rundunar sojojin Najeriya ne ya bayyana haka a jiya Talata.

Janar Onyenma, ya ja kunnen ‘yan siyasar kasar wadanda suke son mulkin kasar ba ta hanyar demokradiyya ba, kan cewa su shiga taitayinsu, domin kuwa sojojin kasar za su ci gaba da kare tsarin demokradiyyar kasar wacce aka girka a shekara 1999, domin a ganinsu shi ne yafi alhairi ga kasar duk da matsalolin tsaron da ake fama da su..

342/